📖 Ayuba 41
-
1
“Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya?
-
2
Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?
-
3
Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali?
-
4
Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?
-
5
Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?
-
6
’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu?
-
7
Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu?
-
8
In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!
-
9
Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne.
-
10
Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?
-
11
Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.
-
12
“Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.
-
13
Wa zai iya tuɓe mata mayafinta? Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta.
-
14
Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta? Haƙoranta ma abin tsoro ne?
-
15
An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai.
-
16
Suna kurkusa da juna yadda da ƙyar iska take iya wucewa tsakani.
-
17
An haɗa su da juna sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba.
-
18
Numfashinta yana fitar da wuta; idanunta kamar hasken zuwan safe.
-
19
Wuta tana fitowa daga bakinta; tartsatsin wuta suna fitowa,
-
20
Hayaƙi yana fitowa daga hancinta kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.
-
21
Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta.
-
22
Akwai ƙarfi a cikin wuyanta; razana tana wucewa a gabanta.
-
23
Namanta yana da kauri a manne da juna; naman yana da tauri ba ya matsawa.
-
24
Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse, da ƙarfi kamar dutsen niƙa.
-
25
Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata; suna ja da baya.
-
26
Takobi ba ta iya yankanta, kibiya ko māshi ba sa iya huda ta.
-
27
Ƙarfe kamar kara ne a wurinta tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta.
-
28
Māsu ba su sa ta tă gudu; jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta.
-
29
Kulki a gare ta kamar ciyawa ne, tana dariyar wucewar māshi.
-
30
Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya.
-
31
Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.
-
32
A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa.
-
33
Ba wani abu kamar ta a duniya, halitta marar tsoro.
-
34
Tana rena duk masu girman kai. Ita take mulki kan duk masu girman kai.”