📖 Ayuba 4
-
1
¶ Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
-
2
“In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru?
-
3
Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi.
-
4
Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu.
-
5
Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.
-
6
Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka?
-
7
“Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka? Ko an taɓa hallaka masu adalci?
-
8
Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta.
-
9
A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su.
-
10
Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki.
-
11
Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci, ’ya’yan zakanya kuma sun watse.
-
12
“Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji.
-
13
Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.
-
14
Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.
-
15
Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi.
-
16
Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.
-
17
‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?
-
18
In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,
-
19
to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!
-
20
Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.
-
21
Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’