📖 Ayuba 39
-
1
“Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
-
2
Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa?
-
3
Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.
-
4
’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa.
-
5
“Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi? Wane ne yake kunce igiyoyinsu?
-
6
Na sa jeji yă zama gidansa ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.
-
7
Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari; ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.
-
8
Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.
-
9
“Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
-
10
Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka?
-
11
Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka?
-
12
Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka?
-
13
“Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
-
14
Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
-
15
ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
-
16
Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
-
17
Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.
-
18
Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
-
19
“Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
-
20
Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
-
21
Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
-
22
Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
-
23
Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
-
24
Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
-
25
Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi.
-
26
“Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?
-
27
Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama?
-
28
Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa.
-
29
Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa.
-
30
’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”