📖 Ayuba 38
-
1
¶ Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,
-
2
“Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi?
-
3
Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini.
-
4
“Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani.
-
5
Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?
-
6
A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,
-
7
yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.
-
8
“Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.
-
9
Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,
-
10
sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa.
-
11
Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?
-
12
“Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito,
-
13
don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?
-
14
Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga.
-
15
An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi.
-
16
“Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?
-
17
Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?
-
18
Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka.
-
19
“Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama?
-
20
Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?
-
21
Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.
-
22
“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara
-
23
waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa?
-
24
Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?
-
25
Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa
-
26
don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki
-
27
don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can?
-
28
Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa?
-
29
Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai
-
30
lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare?
-
31
“Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?
-
32
Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?
-
33
Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?
-
34
“Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?
-
35
Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’
-
36
Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa?
-
37
Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai
-
38
sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya?
-
39
“Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.
-
40
Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?
-
41
Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci?