📖 Ayuba 37
-
1
“Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.
-
2
Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa.
-
3
Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
-
4
Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu.
-
5
Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
-
6
Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
-
7
Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
-
8
Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu.
-
9
Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.
-
10
Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
-
11
Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
-
12
Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi.
-
13
Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
-
14
“Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
-
15
Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
-
16
Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
-
17
Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa,
-
18
ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi?
-
19
“Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa; ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.
-
20
Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana? Ko wani zai nemi a haɗiye shi?
-
21
Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta.
-
22
Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya, Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.
-
23
Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu, shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci, ba ya cutar mutum.
-
24
Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”