📖 Ayuba 36
-
1
¶ Elihu ya ci gaba,
-
2
“Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.
-
3
Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.
-
4
Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.
-
5
“Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.
-
6
Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.
-
7
Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.
-
8
Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,
-
9
yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.
-
10
Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu.
-
11
In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.
-
12
Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi.
-
13
“Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.
-
14
Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.
-
15
Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu.
-
16
“Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so.
-
17
Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye; shari’a da kuma gaskiya sun kama ka.
-
18
Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya.
-
19
Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?
-
20
Kada ka yi marmari dare yă yi, don a fitar da mutane daga gidajensu.
-
21
Ka kula kada ka juya ga mugunta, abin da ka fi so fiye da wahala.
-
22
“An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa?
-
23
Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’
-
24
Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
-
25
Dukan ’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa.
-
26
Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
-
27
“Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama.
-
28
Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace.
-
29
Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
-
30
Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku.
-
31
Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace.
-
32
Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.
-
33
Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa.