📖 Ayuba 35
-
1
¶ Sai Elihu ya ce,
-
2
“Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’
-
3
Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’
-
4
“Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka.
-
5
Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku.
-
6
In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?
-
7
In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?
-
8
Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.
-
9
“Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.
-
10
Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,
-
11
wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’
-
12
Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.
-
13
Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.
-
14
Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi.
-
15
Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta.
-
16
Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”