📖 Ayuba 34
-
1
¶ Sa’an nan Elihu ya ce,
-
2
“Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi.
-
3
Gama kunne yana rarrabe magana kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci.
-
4
Bari mu zaɓi abin da yake daidai, bari mu koyi abin da yake mai kyau tare.
-
5
“Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.
-
6
Ko da yake ina da gaskiya, an ɗauke ni maƙaryaci; ko da yake ba ni da laifi, kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’
-
7
Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa?
-
8
Yana abokantaka da masu aikata mugunta; yana cuɗanya da mugaye.
-
9
Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’
-
10
“Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure.
-
11
Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.
-
12
Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.
-
13
Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?
-
14
In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,
-
15
’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa.
-
16
“In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce.
-
17
Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?
-
18
Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’
-
19
wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.
-
20
Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.
-
21
“Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.
-
22
Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye.
-
23
Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.
-
24
Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu.
-
25
Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.
-
26
Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su,
-
27
domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.
-
28
Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.
-
29
Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,
-
30
yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko.
-
31
“A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.
-
32
Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’
-
33
Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani.
-
34
“Mutane masu ganewa za su ce, masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini,
-
35
‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’
-
36
Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.
-
37
Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”