📖 Ayuba 33
-
1
“Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.
-
2
Zan yi magana; kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.
-
3
Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata; bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.
-
4
Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.
-
5
Ka amsa mini in za ka iya; ka yi shirin fuskanta ta.
-
6
Ni kamar ka nake a gaban Allah; ni ma daga ƙasa aka yi ni.
-
7
Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka.
-
8
“Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa,
-
9
‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi.
-
10
Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa,
-
11
ya daure ƙafafuna da sarƙa; yana tsaron duk inda na bi.’
-
12
“Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.
-
13
Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?
-
14
Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.
-
15
A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,
-
16
mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,
-
17
don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,
-
18
don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.
-
19
“Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,
-
20
yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.
-
21
Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.
-
22
Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.
-
23
Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,
-
24
yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’
-
25
Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi.
-
26
Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.
-
27
Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.
-
28
Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’
-
29
“Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.
-
30
Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.
-
31
“Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana.
-
32
In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini; yi magana, domin ina so in ’yantar da kai.
-
33
Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni; yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”