📖 Ayuba 32
-
1
¶ Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.
-
2
Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.
-
3
Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.
-
4
Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.
-
5
Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.
-
6
¶ Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani.
-
7
Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’
-
8
Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.
-
9
Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.
-
10
“Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani.
-
11
Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,
-
12
na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.
-
13
Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’
-
14
Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.
-
15
“Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa; kalmomi sun kāsa musu.
-
16
Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.
-
17
Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani.
-
18
Gama ina cike da magana, kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;
-
19
a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.
-
20
Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa.
-
21
Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;
-
22
gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.