📖 Ayuba 30
-
1
“Amma yanzu suna yi mini ba’a waɗanda na girme su, waɗanda iyayensu maza ba su isa su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.
-
2
Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni, tun da ba su da sauran kuzari?
-
3
Duk sun rame don rashi da yunwa, suna yawo a gaigayar ƙasa a kufai da dare.
-
4
A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi, jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.
-
5
An kore su daga cikin mutanensu, aka yi musu ihu kamar ɓarayi.
-
6
An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa.
-
7
Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji, suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.
-
8
Mutane marasa hankali marasa suna, an kore su daga ƙasar.
-
9
“Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa na zama abin banza a gare su.
-
10
Suna ƙyamata suna guduna; suna tofa mini miyau a fuska.
-
11
Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala sun raba ni da mutuncina.
-
12
A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar; sun sa tarko a ƙafafuna, sun yi shirin hallaka ni.
-
13
Sun ɓata mini hanyata; sun yi nasara cikin hallaka ni, ba tare da wani ya taimake su ba.
-
14
Suka nufo ni daga kowane gefe; suka auko mini da dukan ƙarfinsu.
-
15
Tsoro ya rufe ni; an kawar mini mutuncina kamar da iska, dukiyata ta watse kamar girgije.
-
16
“Yanzu raina yana ƙarewa; kwanakin wahala sun kama ni.
-
17
Dare ya huda ƙasusuwana; ina ta shan azaba ba hutawa.
-
18
A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina; ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.
-
19
Ya jefa ni cikin laka, na zama ba kome ba sai ƙura da toka.
-
20
“Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba. Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.
-
21
Ka dube ni ba tausayi; Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.
-
22
Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska; ka jujjuya ni cikin hadari.
-
23
Na san za ka sauko da ni ga mutuwa zuwa wurin da kowane mai rai zai je.
-
24
“Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala. Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa.
-
25
Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?
-
26
Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau, mugun abu ne ya zo; Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.
-
27
Zuciyata ba tă daina ƙuna ba; ina fuskantar kwanakin wahala.
-
28
Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba. Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako.
-
29
Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi.
-
30
Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa; jikina yana ƙuna da zazzaɓi.
-
31
Garayata ta zama ta makoki, sarewata kuma ta zama ta kuka.