📖 Ayuba 3
-
1
¶ Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi.
-
2
Ayuba ya ce,
-
3
“A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’
-
4
Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana.
-
5
Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta.
-
6
Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni.
-
7
Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki.
-
8
Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa.
-
9
Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani,
-
10
gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba.
-
11
“Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?
-
12
Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu?
-
13
Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama
-
14
tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,
-
15
da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.
-
16
Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.
-
17
A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta.
-
18
Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.
-
19
Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa.
-
20
“Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai
-
21
ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye,
-
22
waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari?
-
23
Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi.
-
24
Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa;
-
25
Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni.
-
26
Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.”