📖 Ayuba 29
-
1
¶ Ayuba ya ci gaba da jawabinsa,
-
2
“Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can, kwanakin da Allah yake lura da ni,
-
3
lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.
-
4
Kwanakin da nake tasowa, lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,
-
5
lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni, kuma ’ya’yana suna kewaye da ni,
-
6
lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa, duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.
-
7
“Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna a bainin jama’a,
-
8
matasan da suka gan ni sukan ja gefe tsofaffi kuma suka tashi tsaye;
-
9
sarakuna suka yi shiru suka rufe bakunansu da hannuwansu;
-
10
Muryar manya ta yi tsit harshensu ya manne a rufin bakunansu.
-
11
Duk wanda ya ji ni ya yaba mini waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,
-
12
domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
-
13
Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya.
-
14
Na yafa adalci ya zama suturata; gaskiya ita ce rigata da rawanina.
-
15
Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu.
-
16
Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo.
-
17
Na karya ƙarfin mugaye na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.
-
18
“Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana, kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.
-
19
Jijiyoyina za su kai cikin ruwa, kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.
-
20
Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau, bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’
-
21
“Mutane suna mai da hankali su saurare ni, suna yin shiru don su ji shawarata.
-
22
Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba. Maganata ta shige su.
-
23
Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama. Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.
-
24
Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda; hasken fuskata yana da daraja a gare su.
-
25
Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin rundunansu; ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.