📖 Ayuba 28
-
1
Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya.
-
2
Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.
-
3
Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.
-
4
Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi.
-
5
Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;
-
6
akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.
-
7
Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba, ba shahon da ya taɓa ganin ta.
-
8
Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta.
-
9
Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.
-
10
Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.
-
11
Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.
-
12
Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama?
-
13
Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai.
-
14
Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.”
-
15
Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.
-
16
Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.
-
17
Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.
-
18
Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.
-
19
Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.
-
20
“To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?
-
21
An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.
-
22
Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’
-
23
Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,
-
24
Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.
-
25
Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.
-
26
Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,
-
27
sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.
-
28
Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”