📖 Ayuba 27
-
1
¶ Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,
-
2
“Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
-
3
Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
-
4
bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
-
5
Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
-
6
Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.
-
7
“Bari maƙiyana su zama kamar mugaye, masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci.
-
8
Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?
-
9
Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?
-
10
Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
-
11
“Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.
-
12
Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?
-
13
“Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.
-
14
Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.
-
15
Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.
-
16
Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa,
-
17
abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa.
-
18
Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.
-
19
Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.
-
20
Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.
-
21
Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa.
-
22
Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.
-
23
Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.”