📖 Ayuba 26
-
1
¶ Sai Ayuba ya amsa,
-
2
“Yadda ka taimaki marar ƙarfi! Yadda ka ceci marar ƙarfi!
-
3
Ka ba marar hikima shawara! Ka nuna kana da ilimi sosai.
-
4
Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu? Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?
-
5
“Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukan mazauna cikin ruwaye.
-
6
Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe.
-
7
Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
-
8
Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
-
9
Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
-
10
ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
-
11
Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.
-
12
Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
-
13
Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
-
14
Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”