📖 Ayuba 24
-
1
“Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba? Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan?
-
2
Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.
-
3
Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.
-
4
Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.
-
5
Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.
-
6
Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.
-
7
Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.
-
8
Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.
-
9
Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.
-
10
Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.
-
11
Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.
-
12
Ana jin nishin masu mutuwa daga birni, kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako. Amma bai ba wani laifi ba.
-
13
“Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye, waɗanda ba su san hanyoyinsa ba ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba.
-
14
Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi; yă je yă kashe matalauta da masu bukata; a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.
-
15
Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai; yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’ sai kuma yă ɓoye fuskarsa.
-
16
Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.
-
17
Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu; suna abokantaka da razanar duhu.
-
18
“Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.
-
19
Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke, haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi.
-
20
Waɗanda suka haife su za su manta da su, tsutsotsi za su cinye su; ba za a sāke tunawa da mugaye ba amma an sare su kamar itace.
-
21
Suna cutar macen da ba ta da ɗa, suna nuna wa gwauruwa rashin alheri.
-
22
Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi, ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa.
-
23
Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali, amma idanunsa suna kansu.
-
24
Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci, amma kuma za su ɓace; za su fāɗi a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi.
-
25
“In wannan ba haka ba ne, wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?”