📖 Ayuba 23
-
1
¶ Sa’an nan Ayuba ya amsa,
-
2
“Ko a yau, ina kuka mai zafi; hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi.
-
3
Da a ce na san inda zan same shi; da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama!
-
4
Zan kai damuwata wurinsa in yi gardama da shi.
-
5
Zan nemi in san abin da zai ce mini, in kuma auna abin da zai ce mini.
-
6
Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma? Babu, ba zai zarge ni da laifi ba.
-
7
Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa, kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada.
-
8
“Amma in na je gabas, ba ya wurin; in na je yamma, ba zan same shi ba.
-
9
Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa; sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa.
-
10
Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.
-
11
Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa; na bi hanyarsa ba tare da na juya ba.
-
12
Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe.
-
13
“Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi? Yana yin abin da yake so.
-
14
Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini, kuma yana da sauran irinsu a ajiye.
-
15
Shi ya sa na tsorata a gabansa; sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa.
-
16
Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni.
-
17
Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba, duhun da ya rufe mini fuska.