📖 Ayuba 22
-
1
¶ Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
-
2
“Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?
-
3
Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?
-
4
“Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka?
-
5
Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba?
-
6
Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
-
7
Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.
-
8
Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
-
9
Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu.
-
10
Shi ya sa kake kewaye da tarkuna, shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.
-
11
An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
-
12
“Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
-
13
Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a?
-
14
Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’
-
15
Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar da mugayen mutane suka bi?
-
16
An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika, ruwa ya share tushensu.
-
17
Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’
-
18
Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
-
19
“Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi; marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,
-
20
‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
-
21
“Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka.
-
22
Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.
-
23
In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
-
24
Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
-
25
sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
-
26
Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
-
27
Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.
-
28
Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka.
-
29
Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.
-
30
Zai ceci wanda ma yake mai laifi, wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”