📖 Ayuba 21
-
1
¶ Sai Ayuba ya amsa,
-
2
“Ku saurare ni da kyau; bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.
-
3
Ku ba ni zarafi in yi magana, bayan na gama sai ku yi ba’arku.
-
4
“A wurin mutum ne na kawo kukana? Don me ba zan kāsa haƙuri ba?
-
5
Ku dube ni, ku kuma yi mamaki; ku rufe bakina da hannunku.
-
6
Lokacin da na yi tunanin wannan, sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.
-
7
Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa, suna kuma ƙaruwa da iko?
-
8
Suna ganin ’ya’yansu suna girma, suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.
-
9
Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo.
-
10
Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari.
-
11
Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.
-
12
Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.
-
13
Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.
-
14
Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.
-
15
Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?
-
16
Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
-
17
“Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?
-
18
Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska, ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?
-
19
An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!
-
20
Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka; bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.
-
21
Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?
-
22
“Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?
-
23
Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,
-
24
jikinsa ɓulɓul, ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.
-
25
Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai, bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.
-
26
Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa, kuma tsutsotsi za su cinye su.
-
27
“Na san duk abin da kuke tunani, yadda za ku saɓa mini.
-
28
Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan, tenti wurin da mugaye suke zama?’
-
29
Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba? Ba ku kula da labaransu,
-
30
cewa an kāre mugu daga ranar bala’i, an kāre shi daga ranar fushi?
-
31
Wane ne yake gaya masa abin da ya yi? Wane ne yake rama abin da ya yi?
-
32
Za a bizne shi a kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa.
-
33
Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali; dukan jama’a suna binsa, da yawa kuma suna gabansa.
-
34
“Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”