📖 Ayuba 20
-
1
¶ Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
-
2
“Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa domin abin ya dame ni sosai.
-
3
Na ji wani zargin da ka yi mini na reni, kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.
-
4
“Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya,
-
5
mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.
-
6
Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama, kansa kuma yana taɓa gizagizai.
-
7
Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa; waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’
-
8
Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba zai ɓace kamar wahayi da dare.
-
9
Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba; wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.
-
10
Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.
-
11
Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura.
-
12
“Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa,
-
13
ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa,
-
14
duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.
-
15
Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.
-
16
Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.
-
17
Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.
-
18
Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.
-
19
Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.
-
20
“Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba.
-
21
Ba abin da ya ragu da zai ɗauka; arzikinsa ba zai dawwama ba.
-
22
Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa; ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.
-
23
Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi.
-
24
Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe, kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.
-
25
Zai zāre ta daga bayansa, tsinin zai fita daga hantarsa; tsoro zai cika shi;
-
26
duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.
-
27
Sammai za su fallasa laifinsa; duniya za tă yi gāba da shi.
-
28
Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.
-
29
Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.”