📖 Ayuba 19
-
1
¶ Sai Ayuba ya amsa,
-
2
“Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku?
-
3
Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni, kuna kai mini hari na rashin kunya.
-
4
In gaskiya ne na yi laifi, kuskurena ya rage nawa.
-
5
In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,
-
6
sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.
-
7
“Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.
-
8
Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba; ya rufe hanyata da duhu.
-
9
Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina.
-
10
Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare; ya tuge begen da nake da shi kamar itace.
-
11
Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa.
-
12
Rundunarsa ta zo da ƙarfi; suka kafa sansani kewaye da ni, suka zagaye tentina.
-
13
“Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni.
-
14
Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni.
-
15
Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.
-
16
Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.
-
17
Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni.
-
18
Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.
-
19
Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
-
20
Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira.
-
21
“Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.
-
22
Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba?
-
23
“Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi,
-
24
a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada!
-
25
Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.
-
26
Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.
-
27
Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!
-
28
“In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini, tun da shi ne tushen damuwa,’
-
29
sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”