📖 Ayuba 18
-
1
¶ Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
-
2
“Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.
-
3
Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi?
-
4
Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?
-
5
“An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci.
-
6
Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu.
-
7
Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa.
-
8
Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.
-
9
Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam.
-
10
An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
-
11
Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je.
-
12
Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.
-
13
Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.
-
14
An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai.
-
15
Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama.
-
16
Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama.
-
17
An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
-
18
An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya.
-
19
Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.
-
20
Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas.
-
21
Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”