📖 Ayuba 17
-
1
Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana.
-
2
Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
-
3
“Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari. Wane ne zai kāre ni?
-
4
Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
-
5
In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada ’ya’yansa za su makance.
-
6
“Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.
-
7
Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki; jikina ya zama kamar inuwa kawai
-
8
Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro; marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.
-
9
Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.
-
10
“Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa! Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.
-
11
Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so.
-
12
Mutanen nan sun juya rana ta zama dare. A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’
-
13
In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,
-
14
In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
-
15
To, ina begena yake? Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
-
16
Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?”