📖 Ayuba 16
-
1
¶ Sai Ayuba ya amsa,
-
2
“Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!
-
3
Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?
-
4
Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi in da kuna cikin halin da nake; zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi, in kaɗa muku kaina.
-
5
Amma bakina zai ƙarfafa ku; ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.
-
6
“Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.
-
7
Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya.
-
8
Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.
-
9
Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido.
-
10
Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.
-
11
Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.
-
12
Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;
-
13
maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.
-
14
Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.
-
15
“Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.
-
16
Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;
-
17
duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce.
-
18
“Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina!
-
19
Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama.
-
20
Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah;
-
21
a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
-
22
“Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa.