📖 Ayuba 15
-
1
¶ Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
-
2
“Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado ko yă cika cikinsa da iskar gabas?
-
3
Ko zai yi gardama da maganganun wofi maganganu marasa amfani?
-
4
Amma ka ma rena Allah ka hana a yi addu’a gare shi.
-
5
Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce; kana magana kamar mai wayo.
-
6
Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba; maganar bakinka za tă juya a kanka.
-
7
“Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa? Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?
-
8
Kana sauraron shawarar Allah? Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?
-
9
Me ka sani da ba mu sani ba? Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?
-
10
Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu mutanen da sun girme babanka.
-
11
Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?
-
12
Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske,
-
13
har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?
-
14
“Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki, ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?
-
15
In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba, in har sammai ba su da tsarki a idonsa,
-
16
mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa, wanda yake shan mugunta kamar ruwa!
-
17
“Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani; bari in gaya maka abin da na gani,
-
18
abin da masu hikima suka ce, ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba
-
19
(waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar).
-
20
Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala, wahala kaɗai zai yi ta sha.
-
21
Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa ’yan fashi za su kai masa hari.
-
22
Yana jin tsoron duhu domin za a kashe shi da takobi.
-
23
Yana ta yawo, abinci don ungulaye; ya san ranar duhu tana kusa.
-
24
Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi,
-
25
domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,
-
26
ya tasar masa da faɗa da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.
-
27
“Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu kuma yana da tsoka ko’ina,
-
28
zai yi gādon garuruwan da suka lalace, da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki, gidajen da sun zama tarkace.
-
29
Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba, abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.
-
30
Ba zai tsere wa duhu ba; wuta za tă ƙona rassansa, kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.
-
31
Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.
-
32
Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka, kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.
-
33
Zai zama kamar itacen inabi wanda ’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna, kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.
-
34
Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya, wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.
-
35
Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta; cikinsu yana cike da ruɗami.”