📖 Ayuba 14
-
1
“Mutum haihuwar mace kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.
-
2
Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa; kamar inuwa, ba ya daɗewa.
-
3
Za ka zura ido a kan irin wannan ne? Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?
-
4
Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki? Babu!
-
5
An lissafta kwanakin mutum; ka riga ka ɗibar masa watanni, ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.
-
6
Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi, ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa.
-
7
“Aƙalla itace yana da bege. In an sare shi, zai sāke tsira, zai tohu da kyau.
-
8
Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasa kuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa.
-
9
Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu yă yi tsiro kamar shuka.
-
10
Amma mutum yana mutuwa a bizne shi; daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan.
-
11
Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafi sai wurin yă bushe,
-
12
haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba; har sai duniya ta shuɗe mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.
-
13
“Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni!
-
14
In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa? In haka ne zan daure kwanakin da nake shan wahala har su wuce.
-
15
Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.
-
16
Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina amma ba za ka kula da zunubaina ba.
-
17
Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina.
-
18
“Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwa su farfashe su kuma gusa daga wurarensu,
-
19
yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa, haka kake barin mutum ba bege.
-
20
Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace, ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi.
-
21
Ko an martaba ’ya’yansa maza, ba zai sani ba; Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba.
-
22
Zafin jikinsa kaɗai yake ji yana kuka wa kansa ne kaɗai.”