📖 Ayuba 13
-
1
“Idanuna sun ga waɗannan duka, kunnuwana sun ji sun kuma gane.
-
2
Abin da kuka sani, ni ma na sani; ba ku fi ni ba.
-
3
Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye.
-
4
Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!
-
5
In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.
-
6
Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina.
-
7
Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?
-
8
Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa?
-
9
In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?
-
10
Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye.
-
11
Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba?
-
12
Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne.
-
13
“Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.
-
14
Don me na sa kaina cikin hatsari na yi kasada da raina?
-
15
Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa
-
16
lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!
-
17
Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa; bari kunnuwanku su ji abin da zan ce.
-
18
Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi.
-
19
Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.
-
20
“Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;
-
21
Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.
-
22
Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.
-
23
Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina.
-
24
Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?
-
25
Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?
-
26
Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.
-
27
Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.
-
28
“Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye.