📖 Ayuba 11
-
1
¶ Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
-
2
“Duk surutun nan ba za a amsa maka ba? Ko mai surutun nan marar laifi ne?
-
3
Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?
-
4
Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’
-
5
Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba
-
6
yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.
-
7
“Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?
-
8
Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani?
-
9
Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku.
-
10
“In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?
-
11
Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?
-
12
Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.
-
13
“Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,
-
14
in ka kawar da zunubin da yake hannunka, ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba
-
15
shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba; za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.
-
16
Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.
-
17
Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya.
-
18
Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
-
19
Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
-
20
Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba, kuma ba za su iya tserewa ba; begensu zai zama na mutuwa.”