📖 Ayuba 10
-
1
“Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi.
-
2
Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.
-
3
Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?
-
4
Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?
-
5
Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne
-
6
da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?
-
7
Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.
-
8
“Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?
-
9
Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?
-
10
Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.
-
11
Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?
-
12
Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.
-
13
“Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.
-
14
In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.
-
15
Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.
-
16
In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.
-
17
Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina kana ƙara haushinka a kaina; kana ƙara kawo mini hari.
-
18
“Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata? Da ma na mutu kafin a haife ni.
-
19
Da ma ba a halicce ni ba, da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!
-
20
’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne? Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci
-
21
kafin in koma inda na fito, ƙasa mai duhu da inuwa sosai,
-
22
zuwa ƙasa mai duhun gaske, da inuwa da hargitsi, inda haske yake kamar duhu.”