1¶ Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe. “Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai, abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama. Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki, wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.
2“Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina; maganarsa tana a harshena.
3Allah na Isra’ila ya yi magana, Dutsen Isra’ila ya ce mini, ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci, sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,
4yana kama da hasken safiya a safiya marar girgije, kamar haske bayan ruwan sama da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’
5“Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba? Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba? Ba zai kawo ga cikar cetona yă kuma biya duk bukatuna ba?
6Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan da ba a tattara da hannu.
7Duk wanda ya taɓa ƙaya yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi; akan ƙone su inda suke a zube.”
8¶ Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.
9¶ Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,
10amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.
11¶ Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.
12Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.
13¶ A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.
14Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.
15Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”
16Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.
17Sai ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.
18¶ Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.
19Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
20¶ Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
21Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.
22Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.
23Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.