1¶ To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
2gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
3Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
4¶ Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
5Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
6Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
7Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
8Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
9Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
10Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
11Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
12¶ To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.
13Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.
14Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
15Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
16¶ Ku riƙa farin ciki kullum;
17ku ci gaba da yin addu’a;
18ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
19¶ Kada ku danne aikin Ruhu.
20Kada ku rena annabci,
21amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,
22ku ƙi kowace mugunta.
23¶ Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
24Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
25¶ ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.
26¶ Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki.
27¶ Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa.
28¶ Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.