16Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa.
17Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da ’yan’uwansu. Shallum ne babbansu
18da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.
19Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.
20A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.
21Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
22Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci.
23¶ Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti.
24Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu.
25’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai.
26Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah.
27Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya.
28¶ Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su.
29An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji.
30Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin.
31Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa.
32Waɗansu ’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci.
33¶ Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana.
34¶ Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima.
35Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka
36ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
37Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot.
38Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
39Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
40Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika.
41’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz.
42Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
43Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel.
44Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne ’ya’yan Azel maza.